Isa ga babban shafi
Afrika taTsakiya

Faransa ta rage dakarunta a Afrika ta tsakiya

Kasar Faransa ta bayyana rage yawan dakarunta masu aikin samar da zaman lafiya a kasar Jamhuriyar Afrika ta tsakiya zuwa 350, al’amarin da ke nuna cewa kasar da dab da janye dakarunta daga kasar da ke fama da tashin hankali.

Dakarun Faransa za su fice a watan Disemba
Dakarun Faransa za su fice a watan Disemba AFP PHOTO/STR
Talla

Daga yanzu dai rundunar dakarun samar da zaman lafiyar ta Sangaris za ta kasance ne a matsayin wata rundunar wucin gadi daga cikin dakarun samar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya dubu goma sha biyu a kasar da ke fama da yake yaken kabilanci da addini.

A watan Disemba ne shirin aikin wanzar da zaman lafiyar zai kawo karshe.

A watan Maris na 2013 kasar Jamhuriyyar Afrika ta tsakiya ta fada cikin rikici bayan mayakan Seleka sun hambarar da gwamnatin Francois Bozize.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.