Isa ga babban shafi
Afrika ta Tsakiya

Mata 100 aka yi wa Fyade a Afrika ta tsakiya

Sama da mata 100 ne suka bayyana cewa sojojin wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya sun yi lalata da su a jamhuriuyar Afirka ta Tsakiya Babban magakatar da na majalisar Ban Ki-Moon ya ce ya damu matuka a game da wannan batu.

Sojojin wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya a Afrika ta tsakiya
Sojojin wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya a Afrika ta tsakiya MARCO LONGARI / AFP
Talla

Jakadan Birtaniya a Majalisar Dinkin Duniya, Peter Wilson ya ce akwai bukatar gudanar da bincike kan wannan batu domin hukunta masu laifi.

Sannan ya yi kira ga Babban magakatarda na Majalisar Dinkin Duniya da ya dauki matakin da ya dace domin tabbatar da cewa an hukunta wadanda ke da hannu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.