Isa ga babban shafi
Afrika ta tsakiya

Afrika ta tsakiya na cikin hatsari- Touadera

Shugaban Jamhuriyyar Afrika ta tsakiya Faustin-Archange Touadera ya ce har yanzu kasar shi na cikin hatsari saboda yadda wasu yankunan kasar ke hannun kungiyoyi masu dauke da makamai.

Shugaban Afrika ta tsakiya Faustin Archange Touadera
Shugaban Afrika ta tsakiya Faustin Archange Touadera AFP PHOTO/ SIA KAMBOU
Talla

Shugaban ya fadi haka ne a yau Lahadi a yayin da ya ke cika kwanaki 100 da zaben shi a matsayin shugaban kasa.

A watan Fabrairu ne aka zabi Touadera da nufin tabbatar da zaman lafiya a kasar bayan shafe shekaru ana rikici.

Shugaban ya ce zasu yi kokarin bin matakan da suka dace domin ‘yanto kasar tare da taimakon dakarun kasashen Faransa da na Afrika da wasu kasashen duniya da ke aikin wanzar da zaman lafiya a Bangui.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.