Shugaban FIFA zai kawo ziyara Najeriya
Shugaban hukumar kwallon kafa ta duniya Gianni Infantino zai kawo ziyara a Najeriya a cikin wannan watan na Yuli inda zai gana da masu ruwa da tsaki ga sha’anin kwallon kafa a kasashen Afrika, kamar yadda hukumar kwallon Najeriya ta sanar.
Wallafawa ranar:
Shugaban hukumar kwallon Najeriya Amaju Pinnick ya fadi a shafin intanet na NFF cewa Infantino zai sauka Abuja a ranar lahadi 24 ga watan Yuli a ziyarar kwanaki biyu zai kawo a kasar.
Sannan a ziyarar zai gana da shugaban kasa Muhammadu Buhari kafin ya shiga tattaunawa da kungiyar shugabannin kwallon kafa ta kasashen Afrika wadanda zasu kawo ziyara a Najeriya.
‘Yar Afrika da aka zaba a matsayin babbar sakatariyar hukumar FIFA Fatma Samoura, tare da ita ne za su kawo ziyarar da Infantino wanda aka zaba sabon shugaban FIFA a watan Fabrairun bana.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu