Gambia ta tsare mutane uku Saboda zargin Shugaba Yahya Jammeh da nuna Kabilanci
A Kasar Gambia jami'an tsaro sun yiwa wasu mutane uku mummunar azaba saboda sun zargi shugaba Yahya Jammeh da fifita kabilar sa kawai amma ba ya kaunar sauran kananan kabilun kasar.
Wallafawa ranar:
Lauyan mutanen Abdoulie Fatty ya fadi cewa an tsare mutanen uku aka bukaci su sanyan hannu cikin wata takarda inda akayi ta muzguna masu.
Mutanen na iya fuskantar dauri na tsawon shekaru biyu saboda furta cewa Shugaban kasar baya kaunar kabilar Mandigo wadanda yawan su ya kai kashi 41 daga cikin dari na yawan mutan kasar.
Shi kansa shugaban kasar Yahya Jammeh daga kabilar Diola ya fito, wadan da suke cikin kananan kabilun kasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu