RFI ta bukaci Kamaru ta saki Ahmed Abba
Hukumar gudanarwa ta tashar RFI ta bukaci hukumomin kasar Kamaru su gaggauta sakin wakilin Sashen Hausa Ahmed Abba, wanda ya share watanni 10 a tsare. RFI ta fitar da Sanarwar ne a jiya Laraba bayan Ahmed Abba ya sake gurfana a gaban kotu.
Wallafawa ranar:
RFI tace sakamakon gazawar masu shigar da kara wajen gabatar da shaida a game da zargin da ake wa Dan Jaridar, ya kamata ace an sake shi saboda yadda ya ke gudanar da aikinsa a cikin mutunta doka.
Tuni dai Hukumar gudanarwa RFI ta fassara ilahirin rahotanni da hirarrakin da Abba ya rika turowa a matsayin shi na wakilin rediyon a Kamaru, kuma wadannan bayanai ne za su bayar da dama domin kare shi a gaban kotu tare da tabbatar da cewa ya gudanar da aikinsa a cikin ka'ida.
An dai kama Ahmed Abba a ranar 30 ga watan Yulin 2015 a garin Maroua da ke arewacin kasar, kafin daga bisani a kai shi wani wuri inda ake tsare da shi a asirce.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu