MDD ta cirewa Liberia Takunkumin Karshe
Kwamitin Sulhu na MDD ya cire takunkumai na karshe da aka kakkabawa kasar Liberia domin kawo karshen yakin basasar da ta yi fama da shi har zuwa shekara ta 2003.
Wallafawa ranar:
Takunkumai na karshe da aka cirewa kasar sun shafi hanata cinikin makamai ne, sayar da ma’adinin lu’ulu’u da kuma iccen katako.
Jakaden Amurka a kasar David Pressman ya ce wannan mataki ya nuna cewa babu shaka zaman lafiya ya samu a kasar da tun shekarar 1992 take karkashin takunkumai.
Matakin na MDD zai taimakawa kasar ta fannin tattalin arzikinta, bayan shafe tsawon shekaru 13 da hana ta cinikkaya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu