Isa ga babban shafi
Najeriya-Birtaniya

Buhari zai halarci taron yaki da cin hanci a London

Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari da takwarorinsa na  Afghanistan da Colombia na daga cikin shugabanin kasashen duniya da za su halarci taron duniya kan yaki da cin hanci da rashawa a birnin London, wanda Firaminista David Cameron da Sakataren harkokin wajen Amurka, John Kerry za su jagoran ta.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a gaban majalisar dokokin kasashen Turai
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a gaban majalisar dokokin kasashen Turai REUTERS/Vincent Kessler
Talla

Rahotanni sun ce Firaminista David Cameron na bukatar mahalarta taron su sanya hannu kan wata yarjejeniya wadda za ta tabbatar da ta’adin da matsalar cin hanci ke haifarwa da kuma alkawarin magance ta.

Cameron ya ce, a baya, yaki da cin hanci da rashawa na da matukar wahala, saboda haka wannan taron zai sauya wancan matsayi, kuma mahalartansa za su daga darajar yaki da annobar da ta damu duniya yanzu haka.

Cikin mahalarta taron sun hada da shugaban Najeriya, Muhamamdu Buhari da shugaban Afghansitan, Ashraf Ghani da na Colombia Juan Manuel Santos da Firaminsitan Norway Erna Solberg.

Sauran sun hada da shugabar hukumar bada lamuni ta duniya, Christine Lagarde da shugaban Bankin Duniya Jim Yong Kim da shugaban kungiyar Transparency, Jose Ugas da mataimakin Firaminsita Rasha, Oleg Syromolotov.

Cameron ya ce taron zai kuma tattauna matsalar cin hanci a bangaren wasanni.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.