Isa ga babban shafi
Chadi

Idriss Deby ya lashe zaben Chadi

Shugaba Idriss Deby Itno ya lashe zaben shugabancin kasar Chadi da aka gudanar a ranar 10 ga watan Afrilu bayan da ya samu sama da kashi 61 na kuri’un da aka jefa.

Shugaban Chadi Idriss Deby
Shugaban Chadi Idriss Deby REUTERS
Talla

Tsohon mai adawa da shugaba Deby Saleh Kebzabo ya zo a matsayin na biyu da kusan kashi 12 cikin dari yayin da magajin garin Moundou da ke kudancin kasar Laoukein Kourayo Medard ya samu kashi 10 cikin dari a zaben.

Hukumomin Zaben sun bayyana cewa an samu fitowar kashi 71 na wadanda suka cancanci jefa kuri’unsu.

Tuni dai aka yi has ashen Idriss Deby ne zai lashe zaben wanda tun 1990 ya ke shugabanci a wani juyin mulkin Soji.

Nan da kwanaki ne dai kotun kundin tsarin mulki za ta amince da sakamakon zaben wanda ‘Yan adawa ke zargin an yi magudi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.