Isa ga babban shafi
Chad

Jami'an tsaron Chadi sun kama Bafaranshe

Jami’an tsaron kasar Chadi sun kama wani Bafaranshe Thomas Dietrich, da ke nuna adawa ga gwamnatin kasar bayan isarsa a birnin N’Djamena a ranar Assabar da ta gabata.

Jami'an tsaron Chadi sun kama Bafaranshen da ke adawa da gwamnatin kasar
Jami'an tsaron Chadi sun kama Bafaranshen da ke adawa da gwamnatin kasar AFP/AFP/Archive
Talla

Shi dai Thomas Dietrich da ke nuna tsananin adawa ga gewamnatin Idris Deby, tun a birnin Paris ofishin jakadancin kasar Chadi ya hana shi Bisar shiga kasar amma sai ya bi ta Yaoundén kasar Kamaru inda ya samu Bisar, inda a jiya Litanin 'yan sandan siyasa suka dakatar da shi.

A cikin wani sako da ya yada ta Facebook  Thomas Dietrich ya bayyana ziyararsa a N'Djamena tare da bayyana irin mulkin danniya da take hakkin dan Adam da ya ce gwamnatin kasar na yi, ya kuma fadi haka ne a matsayin bada tasa gudunmawa ga al’ummar kasar da ke kukan yunwa duk kuwa da arzikin man fetur din da kasar ke da shi.

Shugaban kasar Idriss Deby Itno da ya share tsawon shekaru 26 kan karagar shugabancin kasar inda ya sake tsayawa takarar shugabancin kasar karo na 5 a zaben da aka gudanar a ranar 10 ga wannan wata na Aprilu, zaben da yanzu haka aka share tsawon mako guda ana dakon sakamakonsa.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.