Isa ga babban shafi
Benin

Talon ya yi alkawalin yin wa’adi guda a Benin

Sabon Shugaban kasar Jamhuriyar Benin Patrice Talon ya shaidawa al’ummar kasar aniyarsa na yin wa’adin mulki guda, duk da yana da ‘yancin sake neman wa’adi na biyu kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar ya tanada.

An rantsar da  Patrice Talon a matsayin sabon shugaban Benin
An rantsar da Patrice Talon a matsayin sabon shugaban Benin YANICK FOLLY / AFP
Talla

Wannan dai shi ne karo na biyu da shugaban ke bayyana bukatar ganin an sauya kundin tsarin mulkin kasar don shata wa’adi guda ga duk wani shugaba.

A jiya Laraba ne aka rantsar Talon bayan ya lashe zaben shugaban kasa da aka gudanar watan jiya.

Talon ya karbi ragamar tafiyar da Benin daga Thomas Boni Yayi bayan wa’adin shugabancin shi ya kawo karshe.

A cikin jawabin shi bayan rantsuwa Talon ya yi wa jama’ar Benin alkawalin yin shugabanci na nagari tare da inganta rayuwarsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.