Isa ga babban shafi
Holland

An kama wani dan ta'adda a Holland

Masu shigar da kara a Holland sun ce ‘Yansanda sun gano tarin alburusai a gidan wani dan asalin kasar Faransa mai suna Anis B. da aka Cafke a birnin Rotterdam kan zargin  kitsa kai hari a kasar Faransa

Walid Lakdim da Bilal El Makhoukhi,Wasu wadanda ake zargi da hannu a harin Belgium
Walid Lakdim da Bilal El Makhoukhi,Wasu wadanda ake zargi da hannu a harin Belgium REUTERS/Francois Lenoir
Talla

Anis B mai shekaru 32 dai tun a jiya lahadi aka cafke shi, kuma ake zarginshi da karba umarni daga ISIL don kai hari Faransa, akwai kuma Reda Kriket dake hannun jami’an tsaro bayan cafke shi a waccan makon lokacin da yayi kokarin kai hari birnin Paris

Mai magana da yawun masu shigar da kara a Netherland Wim De Bruin ya ce an gano wasu wayoyin hannu, da katin waya da kundin adana bayanai na na’ura mai kwakwalwa, dama kudade da alburusai da kuma kwayoyi a samame da jami’an tsaro suka kai gidan Anis

Sai dai kuma ba'a tsinci abubuwan fashewa ba, an kuma cafke mutane 4, cikinsu harda wani dan kasar Algeria bisa zargin kitsa ayyukan ta'addanci.

De Bruin ya ce ana saran a mikawa Faransa Anis B bayan kammala sauraron hukuncin kotun Amsterdam

Tun bayan harin Brussels, hukumomin Netherlands suka tsaurara matakan tsaro a iyakokin kasar da filin tashin da saukan jirgi tare da fadada samame a kusurwar kasar don gano ‘yan ta’adda.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.