Isa ga babban shafi
Benin

An Fara Zaben Shugaban Kasa a Benin

Mutane miliyan hudu da dubu dari bakwai na zaben shugaban kasa a Benin yau Lahadi, kuma bayanai na nuna an fara zaben cikin nasara ba tare da wani tashin hankali ba. 

Shugaban Benin Thomas Boni Yayi
Shugaban Benin Thomas Boni Yayi SEYLLOU / AFP
Talla

An jinkirta wannan zabe da makonni biyu saboda Hukumar zabe dake kasar ta sami kammala dukkan shiri da suka wajaba.

Majiyoyin samun labarai na cewa an bude rumfunan zabe tun misalin karfe shida na safe kuma akwai alamun jama'a za su fito domin jefa kuri'ar su.

Akwai ‘yan takara 33 dake neman hawa kujeran shugabancin kasar.

Shugaban kasar mai ci Thomas Boni Yayi ba ya cikin neman zarcewa da iko bayan ya kammala wa’adin sa na biyu na tsawon shekaru goma.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.