Isa ga babban shafi
MDD

Tsohon magatakardar na MDD Boutros Boutros-Ghali ya rasu

Majalisar Dinkin Duniya ta sanar da rasuwar tsohon Sakatarenta Boutros Boutros Ghali wanda ya rasu yana da shekaru 93 a duniya,Boutros-Ghali ya shugabanci Majalisar tsakanin shekarar 1992 zuwa 1996.  

Tsohon magatakarda na MDD, Boutros Boutros-Ghali
Tsohon magatakarda na MDD, Boutros Boutros-Ghali
Talla

Shugaban kwamitin Sulhu na Majalisar kuma Jakadan Venezuela Rafael Dario Ramirez Carreno ne ya sanar da rasuwar abinda ya sa wakilan kwamitin 15 suka tsaya tsit na minti guda dan nuna alhinin su.

Rahotanni sun ce Boutros-Ghali ya rasu ne a asibitin Al Salam dake Birnin Alkahira dake kasar Masar.

Duniya zata tuna wa’adin Boutros-Ghali a Majalisar wadda ta kunshi yaki a tsohuwar kasar Yugoslavia da kuma yunwar da aka samu a Afirka da kuma kisan kare dangi, sai kuma karon da yayi da kasar Amurka.

A matsayin sa na Sakatare Janar na farko da ya fito daga Afirka, Boutros-Ghali ya danganta kan sa da yunwar da aka samu a Somalia abinda ya sa ya shirya gidauniya ta musamman dan tallafawa al’ummar kasar.

Yunkurin sa na kawo sauyi a cibiyar Majalisar da kuma daidaita ma’aikata yasa aka masa lakabi da suna Fir’auna, kana karo da manufofin Afirka ya sa kasar taki amincewa ta biya Karin kudin tallafin da take bayar wa na dala biliyan guda, abinda ya sa gwamnatin shugaba Bill Clinton ta bukaci sauya shi lokacin da ya nemi wa’adi na biyu, duk da goyan bayan wakilan kwamitin sulhu 10 da ya samu.

Shi dai Boutros-Ghali ya fito daga gidan masu hannu da shuni a Masar, kuma kakan sa ya taba rike mukamin Firaministan kasar kafin kisan gillar da aka masa a shekarar 1910.

Kafin zama Sakatare Janar, Boutros-Ghali yayi aiki da gwamnatin shugaba Anwar Sadat da Hosni Mubarak, kuma ya taba rike mukamin Sakataren kungiyar kasashe renon Faransa da ake kira Francophonie.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.