Isa ga babban shafi
Burundi

An saki 'yan jaridun Birtaniya da Faransa a Burundi

Hukumomi a kasar Burundi sun sallami wasu ‘yan jaridu biyu, wato Bafaranshe Jean-Philippe Rémy da kuma dan kasar Birtaniya Phil Moore wandada aka kama ba tare da an tuhume su da aikata wani laifi ba. 

'Yan jaridun Faransa da  na Birtaniya da aka kama a  Burundi Jean-Philippe Rémy da Phil Moore.
'Yan jaridun Faransa da na Birtaniya da aka kama a Burundi Jean-Philippe Rémy da Phil Moore. CHARLY TRIBALLEAU, PHIL MOORE / AFP
Talla

An dai saki mutanen biyu ne bayan sun share tsawon sa’o’i 24 a hannun jami’an tsaro.

Jean-Philippe Rémy wanda ke aiki da jaridar Le Monde da Phil Moore wanda ke wa kafafen labarai na New York Times, The Guardian da kuma Der Spiegel aiki, an gabatar da su ne a gaban alkali a tsakiyar ranar wannan jumma'ar, to  sai dai kafin nan sun sha tambayoyi da dama daga jami’an hukumar tara bayanan sirri ta kasar.

Jakadan Faransa a Burundi Gerrit Van Rossum, ya tabbatar da cewa an sallami mutanen ba tare a wani caji ba, amma ya ce ba a mayar masu da kayayyakinsu na aiki ba.

Tsare 'yan jaridun biyu dai ya gamu da kakkausar suka daga ciki da wajen kasar ta Burundi, kasar da yanzu haka kungiyoyi masu zaman kansu ke zargi da tauye hakkokin bil Adama.

Yanzu haka dai taron share fage na kungiyar tarayyar Afrika da ke gudana a birnin Adis Ababa na Habasha a wannan juma’a na tattaunawa kan yiyuwar aikewa da dakarun wanzar da zaman lafiya a kasar, lura da halin da ake ciki wanda manazarta ke cewa akwai yiyuwar barkewar yakin basasa a can.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.