Isa ga babban shafi
Faransa

Direbobin Taxi a Faransa na yajin aiki

Matafiya ta jiragen sama da ma su amfani da motocin sufuri ko taxi a kasar Faransa na fuskantar wahaloli yau Talata sakamakon yajin aiki da ma’aikantan sufuri suka shiga.Daga jiya litinin ne aka soke zirga-zirgen jiragen sama akalla kashi 20%  a kasar Faransa don fargaban yajin aikin na yau.

Motocin sufuri ko Taxi a gaban wani Otel
Motocin sufuri ko Taxi a gaban wani Otel AFP PHOTO/PANTA ASTIAZARAN
Talla

Yajin aikin yan taxi na yau talata zai yi tasiri ganin yadda tuni kungiyar matuka jiragen kasa a kasar, suke cikin yajin aikin neman hakkokinsu na ritaya, tare da neman hakkin daya daga cikinsu da aka ciwa zarafi.

Kungiyar yan taxi ta tsunduma cikin yajin aikin ne sakamakon nuna rashin amincewa da kamfanin masu motocin yawon bude ido dauke da direba bayan gwagwarmayar da suka sha kan kamfanin Uber na kasar Amurka a baya.
Shugaban kungiyar Taxi G7 Serge Metz ya yi alkawalin matsantawa a yajin aikin na yau, inda ya bayyana cewa za su dasa shingayen binciken gano direbobin taxi da zasu yi bris da kiran kungiyar

Masu hasashe na ganin birnin Paris nan ne yajin aikin zai fi haifar da matsala musaman a yankin filayen tashi da saukar jirage na Roissy da ’Orly.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.