Isa ga babban shafi

‘Yan Majalisun Faransa sun amince da dokar gyara bangaren sufuri

‘Yan Majalisa a kasar Faransa sun amince da dokar gyara bangaren sufurin jirgin kasa da ya sha suka daga ma’aikata masu yajin aikin da ya durkusar da ayyukan Jiragen kasa a kasar a makon jiya.

Shugaban kasar Faransa, Francois Hollande
Shugaban kasar Faransa, Francois Hollande REUTERS/Philippe Wojazer
Talla

Mambobin majalisar wakilan kasar ta Faransa dai sun jefa kuri’u domin amincewa da yin gyara ga dokar hada ma’aikatan sassa daban daban na bangaren sufurin jirgin kasa.

Shugaban kasar Faransa Francois Hollande, na jam’iyyar Socialist ya goyawa kudurin dokar baya da ‘yan Majalisar suka amince da shi da kuma wasu mambobin jam’iyyar hamayya ta UMP.

Ana dai shirin daukar wannan matakin ne domin ragewa sashen sufurin jirgin kasar dimbin bashin da yake fama da shi ne da ya kai Euro Billiyan 40.

Wasu daga cikin kungiyoyin ma’aikatan jiragen kasa dai sun amince tare da rattaba hannu ga dokar, a yayin da biyu daga cikinsu suka ki, tare da bayyana cewar daukar matakin kan iya haddasa rashin ayyukan yi.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.