Kura ta lafa a Tunisiya bayan barkewar zanga zanga a kasar
Frayi ministan kasar Tunisiya Habib Essid ya bukaci al’ummar kasar da su kai zukata nesa, mako guda bayan barkewar zanga zangar al’umma kan tsadar rayuwa, irinta mafi muni da akasamu tun bayan abkuwar wace ta assasa juyin juya halin kasashen larabawa a 2011
Wallafawa ranar:
Habib Essid ya yi wannan kira ne, ba tare da bayyana daukar wasu jerin kwararan matakan magance zaman kashe wondo da cin hanci da rashawar da suka yiwa kasar katutu ba.
Zaman taron majalisar ministocin da aka gudanar a jiya assabar a birin Tunis babban birnin kasar, ya bayyana samun lafawar tarzoma a ko ina cikin fadin kasar ta Tunisiya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu