Kagame ya yi watsi da furunci Amurka kan takararsa
Shugaban Rwanda Paul Kagame ya yi watsi da sukar da kasar Amurka ta yi masa, bayan da ya sanar da aniyarsa ta tsayawa takarar shugabancin kasar karo na uku.
Wallafawa ranar:
Kagame wanda ke mayar da martani a shafinsa na Twitter, ya ce furucin da ma’aikatar wajen Amurka ta fitar dangane da tsayawarsa takara, kalamai ne da aka taba jin irinsu sau da dama, kuma ba za su taba magance matsalar Nahiyar Afirka ba.
Amurka dai na gani cewa tsayawar takarar Kagame a wa’adi na uku kuskure ne da zai karya lagon demokradiyar kasar, domin salon mulkin kama karya yake shirin aiwatarwa a kasar, musamman lura da yadda jam’iyyun adawa kasar ba sa wani tasiri.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu