Isa ga babban shafi
Najeriya

Sojojin Najeriya sun kashe ‘Yan Boko Haram 10 a Maiduguri

Sojojin Najeriya sun kashe wasu da ake tunanin ‘Yan Boko Haram ne da suka yi yunkurin kai hare haren kunar bakin wake a garin Maiduguri na Jihar Borno a jiya Lahadi.

Sojojin Najeriya na fada ne da Boko Haram tare da hadin guiwar dakarun Chadi da Nijar da Kamaru da Benin
Sojojin Najeriya na fada ne da Boko Haram tare da hadin guiwar dakarun Chadi da Nijar da Kamaru da Benin REUTERS/Emmanuel Braun
Talla

Rahotannni sun ce an ji karan harbe harbe da fashe fashe a sassan birnin Maiduguri abin da ya tada hankalin jama’a.

Kakakin rundunar Sojin ta Zaman Lafiya Dole Kanal Mustapha Anka yace sojojinsu ne suka murkushe wasu da ke shirin kai harin kunar bakin wake a Ajiri da ke hanyar Damboa, da wasu wurare uku kuma kimanin 10 daga cikinsu aka kashe 10.

A sanarwar da ya fitar Kanar Anka ya bukaci mutanen yankin su kwantar da hankalinsu, domin jami’ansu na ci gaba da bincike domin tabbatar da sun zakulo sauran maharan.

Wasu rahotanni sun ce Sojojin sun yi kokarin hana wa mayakan ne shiga Maiduguri daga Kauyen Aladuwari.

Babu dai cikakken bayani akan adadin fararen hula da aka kashe a musayar wutar da aka yi tsakanin Sojojin da mayakan na Boko Haram.

A ranar Lahadi rahotanni sun ce ‘Yan Boko Haram sun shiga kauyen Jiddari Polo da safe inda suka yi ta harbe harbe.

Wannan kuma na zuwa ne a yayin da gwamnatin Najeriya ke ikirarin samun nasarar kawo karshen Boko Haram.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.