Isa ga babban shafi
Najeriya

Najeriya za ta rage farashin Man fetir zuwa 85

Gwamnatin Najeriya za ta rage farashin man fetir zuwa Naira 85 daga ranar daya ga watan Janairun sabuwar shekarar 2016 da zamu shiga. Farashin zai sauka daga Naira 87 zuwa 85 kamar yadda Ministan kasa na man fetir Emmanuel Kachikwu ya tabbatar wa manema labarai a garin Fatakwal.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari. REUTERS/Afolabi Sotunde
Talla

Ministan yace tun a ranar Alhamis ne ya sanya hannu kan matakin, kuma zuwa 1 ga watan Janairu tsarin zai fara aiki.

Tuntuni ne ake hasashen gwamnatin Najeriya zata rage farashin fetir saboda faduwar danyen mai a kasuwannin duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.