Isa ga babban shafi
Najeriya

Dalilin da ya sa Sojoji suka murkushe ‘Yan Shi’a a Zaria

Rundunar Sojin Najeriya ta bayyana dalilin da ya sa Jami’anta suka murkushe almajiran shugaban mabiya Shi’a Ibrahim Zakzakky a garin Zaria a Jihar Kaduna a arewacin kasar.

Kakakin rundunar Sojin Najeriya Kanal Usman Kukasheka
Kakakin rundunar Sojin Najeriya Kanal Usman Kukasheka via twitter
Talla

A cikin wata sanarwa da rundunar Sojin ta fitar a ranar Lahadi, kakakinta Sani Usman Kukasheka ya daura laifin faruwar al’amarin da ya kai ga rasa rayukan mutane da dama akan ‘Yan Shi’a da suka toshe hanya tare da hanawa mutane gudanar da ayyukansu na yau da kullum.

A ranar Assabar ne mabiya Shi’a suka toshe hanya a kusa da Husainiyya cibiyarsu a Zaria.

“Kundin tsarin mulki ya ba mutane damar gudanar da gangami ko zanga-zanga amma cikin lumana, sannan ya ba mutane ‘yancin walwala a hanyoyin kasar da aka samar domin su.” a cewar Kukasheka.

Tuni rundunar Sojin ta Najeriya ta zargi almajiran Zakzakky da yunkuri halaka babban Hafsan Sojin kasar Janar Yusuf Burutai, a lokacin da ye kan hanyar isa fadar Sarkin Zazzau.

Amma shugaban mabiyan Ibrahim Zakzakky ya karyata ikirarin a zantawarsa da RFI Hausa.

"Mun shafe shekaru 37 muna harakarmu ba tare da kai wa wani hari ba" a cewar Zakzakky."

Kakakin kungiyar ‘Yan Shi’a Ibrahim Musa ya ce mabiyansu da dama ne Sojoji suka kashe ciki har da mataimakin Zakzakky.

Wasu Rahotanni kuma na cewa akwai matar Zakzakky cikin wadanda Sojoji suka kashe a rikicin na Zaria bayan sun abkawa gidansa a Gyallesu.

Babu dai cikkakken bayani daga Sojin Najeriya akan yawan adadin wadanda suka mutu da kuma makomar shugaban ‘Yan Shi’ar Ibrahim Zakzaky.

Wasu rahotanni na cewa Sojoji sun kame shi.

Kanal Usman Kukasheka yace ‘Yan sanda za su gudanar da bincike kan faruwar lamarin, kuma za a sanar da ‘Yan Najeriya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.