Isa ga babban shafi
Tunisia-Libya

Tunisia ta rufe iyakar ta da Libya

Gwamnatin Kasar Tunisia ta sanar da cewar za ta rufe iyakar kasar ta da Libya na kwanaki 15 kwana guda bayan kazamin harin da ya hallaka jami’an tsaron fadar shugaban kasar 13 wanda tuni kungiyar ISIS ta dauki alhakin kai harin.

France 24
Talla

Majalisar tsaron kasar a karkahsin shugaban kasa Beji Essebsi ta dauki matayin rufe iyakar daga daren Yau da kuma karfafa matakan tsaro na ruwa da tashar jiragen sama da kuma rufe kafofin intanet da ke da alaka da ayyukan ta’addanci.

Majalisar ta kuma sanar da shirin daukar ma’aikatan liken asiri 3,000 da sojoji 3,000 a cikin shekara mai zuwa.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.