Isa ga babban shafi
Tunisia

Majalisar dokokin Tunisia ta amince da sabuwar dokar yaki da Ta’addanci

‘Yan majalisar dokokin kasar Tunisia sun kada kuri’ar amincewa da wata sabuwar dokar yakin da ayyukan ta’addanci a kasar,daga ladabtarwa, har ya zuwa ga hukuncin kisa.

REUTERS/Zoubeir Souissi
Talla

Amincewa da dokar na zuwa ne duk kuwa da adawar da kungiyoyin kare hakkin dan adam suka nuna a kan samar da dokar hukuncin kisa a cikin kasar

Tun a jiya laraba ‘Yan majalisar dokokin suka yi nazarin kudrori 33 daga cikin 139 da suka tanadi kafa dokar yaki da ta’addancin

Kuma uku daga cikin kudurorin dokar da ‘yan majalisar suka amince da su ne suka tanadi hukuncin kisan ga duk wanda aka kama da alaka da kungiyoyin ta'addanci ko aikata ta'addancin.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.