Ana zaben gwamnan jihar Kogi a wannan asabar
Rundubnar ‘yan sandan tarayyar Najeriya ta sanar da takaita zirga-zirga a duk fadin jihar Kogi da ke tsakiyar kasar, domin tabbatar da cewa an gudanar da zaben gwmana da ake gudanarwa a wannan asabar.
Wallafawa ranar:
Babban sufeton ‘yan sandan kasar Solmon Arase ya bayyana a wata sanarwa cewa an hana zirga-zirgar ababan hawa daga karfe 6 na safe zuwa 6 na marecen yau asabar hatta ga masu ratsa jihar zuwa wasu yankuna na Najeriya.
An dai tsaurara matakan tsaro a wannan zabe da ake karawa tsakanin gwamnan jihar mai-ci Idris Wada na jam’iyyar PDP da kuma Abubakar Audu na jam’iyyar APC.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu