Saliyo
An kawar da cutar Ebola a Sierra Leone
Hukumomin kiwon lafiya a kasar Saliyo sun ce an kawo karshen cutat Ebola a kasar, bayan da aka share tsawon kwanaki 42 ba tare da an samu wani da ya kamu da ita ba a duk fafin kasar.
Wallafawa ranar:
Talla
A wannan asabar shugaban kasar Bai Koruma na jagoranci wani gagarumin biki domin murnar kawo karshen annobar, wadda a cikin shekaru biyu ta yi sanadiyyar mutuwar mutane sama da dubu hudu a kasar.
Bayan kawo karshen cutar a Sierra Leone, a yanzu dai hankula sun karkata ne zuwa ga kasar Guinee Conakry wadda ita ma ke fama da cutar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu