Isa ga babban shafi
Equatorial Guinea

Equatorial Guinea ta rufe iyakokin ta saboda zaben dan takarar

Hukumomi a Equatorial Guinea sun bayar da umurnin rufe iyakokin kasar har zuwa ranar 15 ga wannan wata na nuwamba domin bai wa jam’iyya mai mulkin kasar damar zaben wanda zai tsaya ma ta takara a zaben shekara mai zuwa.

Shugaban kasar Guinée Equatoriale Severo Moto
Shugaban kasar Guinée Equatoriale Severo Moto AFP PHOTO / Javier Soriano
Talla

Ma’aikatar tsaron cikin gidan kasar ta Guinea ta bayyana cewa iyakokin kasar za su ci gaba da kasancewa a rufe har sai bayan jam’iyyar ta PDGE mai mulki ta kammala taron wanda zai tsaya ma ta takara tsakanin ranar 10 zuwa 12 ga wannan wata a birnin Bata fadar mulkin kasar.

Shugaban kasar Teodoro Obieng Nguema, wanda ya share shekaru 36 kan karagar mulki, bisa ga al’ada shi ne ya saba tsaya wa jam’iyyar takarar shugabancin kasar, yayin da ko a wannan karo ake kyautata zaton cewa shi ne zai sake tsayawa jam’iyyar.

Idan har kuwa shugaban ya yi wa al’ummar kasa ba za ta ta hanyar kin tsayawa takara a zaben mai zuwa, to wasu bayanai na nuni da cewa da ya daga cikin ‘yayansa wanda ke rike da mukamin shugaban matasa na jam ‘iyyar ta PDGE zai iya maye gurbinsa.

Yanzu haka dai mafi yawa daga cikin madafan iko a jam’iyyar na hannun ‘yan uwan shugaba Nguema ne, domin ko baya ga dansa da ke rike da mukamin shugaban matasa, hakazalika matar shugaban ce ke a matsayin shugabar mata ta kasa a jam’iyyar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.