Isa ga babban shafi
Najeriya

Direbobin manyan motoci sun ki janye yajin aiki a Lagos

Masu motocin dakon kaya a Najeriya, sun bukaci magoya bayansu da su kaurace wa zuwa birnin Lagos, sakamakon dokar hana zirga-zirgar manyan motoci daga karfe 6 na safe zuwa 9 na dare da aka kafa a birnin da ke yankin kudu masu yammacin kasar.

Wasu manyan motocin dakon kaya a unguwar Apapa da ke birnin Lagos
Wasu manyan motocin dakon kaya a unguwar Apapa da ke birnin Lagos NAN
Talla

A ganawarsa da manema labarai bayan wata tattaunawa da hukumomin jihar Lagos kan wannan batu, sakataren zartaswa na kungiyar masu motocin dakon kaya Aloga Abogbo, ya bukaci direbobin da su dakatar da zuwa Lagos sai abinda hali ya yi.

Gudanar da zirga-zirga tsakanin karfe 9 na dare zuwa shida na safe, abu ne mai matukar hatsarin ta fannin tsaro a cewar Alhaji Danlami Potislum daya daga cikin shugabannin direbobin.

Shi dai wannan mataki na hana zirga-zirga a rana sam bai shafi masu manyan motocin daukar kasa da ke Lagos ba, abin da kuma Alh Isa Umar Sakatare na bangaren masu shigo da kayan gwari ke cewa tamkar bambanci ne ake nuna masu.

Direbobi da masu motocin dakon kayan, sun bukaci gwmanatin Tarayya da tsoma baki domin janye matakin na Jihar Lagos.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.