Isa ga babban shafi
Swaziland

Mutane 13 sun mutu akan hanyar zuwa bikin Sarauniyar Kyau a Swaziland

Akalla mutane 13 suka mutu kuma akasarin su ‘yan mata ne da ke kan hanyar zuwa bikin zaben macen da tafi kyau da Sarki Mswathi na Swaziland zai aura a matsayin matarsa ta 15.

'Yan Mata na shirye shiryen bikin Sarauniyar Kyau domin Sarki ya zabi guda
'Yan Mata na shirye shiryen bikin Sarauniyar Kyau domin Sarki ya zabi guda AFP PHOTO/GIANLUIGI GUERCIA
Talla

Mai Magana da yawun ‘Yan Sandan kasar Khulekani Mamba ya ce cikin adadin mutanen da suka mutu, 11 ‘Yan mata ne da ke kan hanyarsu ta zuwa bikin zaben wadda ta fi kyau da sarkin zai aura.

Rahotanni sun ce an yi hatsarin ne ranar juma’a da daddare lokacin da motar safar da suke ciki ta yi taho-mu-gama da wata karamar mota tsakanin birnin Mbabne da Manzini.

A yau Litinin da ake saran gudanar da bikin wanda kan janyo dubban ‘Yan Mata da ke neman ganin Sarki ya zabe su.

Sarki Mswathi dai yanzu haka yana da mata 14.

Sai dai wasu bayanai na dabam sun ce ke adadin matan da suka mutu ya haura 30.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.