Isa ga babban shafi
Afrika

Shugabannin Afrika na son yin tazarce

Majalisar dokokin Rwanda tace akasarin al’ummar kasar na goyon bayan matakin yi wa kundin tsarin mulkin kasar kwaskwarima domin ba Shugaba Paul Kagame damar neman wa’adin shugabanci na uku.

Shugaban kasar Rwanda Paul Kagame .
Shugaban kasar Rwanda Paul Kagame . REUTERS/Ruben Sprich
Talla

Wani rahoto da aka fitar a yau Talata ya ce ‘Yan majalisar sun zagaye kasar domin jin ra’ayin jama’a kan matakin canza kundin tsarin mulki.

Tun a watan jiya ne ‘Yan majalisar suka fara zagaye sassan Rwanda domin jin ra’ayin jama’a kan kuri’ar da suka jefa ta amincewa da matakin yi wa kundin tsarin mulkin kasar kwaskwarima domin ba shugaba Paul Kagame neman wa’adin shugabanci na uku.

A cikin wani rahoto da Jaridun Rwanda suka wallafa, ‘Yan majalisar sun ce mutane 10 ne kawai a fadin kasar ke adawa da matakin sauya kundin tsarin mulkin kasar.

A yau Litinin ne kuma ‘Yan majalisar suka mika sakamakon rahoton su na tuntuba ga Majalisa kan sauya sashe na 101 da ke magana kan adadin shekarun shugabanci a kasar.

Kagame ya shafe shekaru sama da 10 yana shugabanci a Rwanda, tun lokacin da aka kawo karshen rikici tsakanin mayakan Hutu da ‘Yan tutsi.

matakin zarcewar Kagame dai na tabbatar da yadda shugabannin Afrika ke kankanewa basu son sauka daga madafan iko.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.