Isa ga babban shafi
Burundi

An gano wadanda suka hallaka wani janar din sojan kasar Burundi

Yau masu gabatar da kara a kasar Burundi suka ce an gano wasu mutanen da ake zargin su suka kashe wani janar din soja mai biyayya ga Pierre Nkurunziza, kuma tuni aka kama da yawa daga cikinsu.

'Yan kasar Burundi suna zanga zangar mutuwar Janar Adolphe Nshimirimana
'Yan kasar Burundi suna zanga zangar mutuwar Janar Adolphe Nshimirimana AFP PHOTO / GRIFF TAPPER
Talla

Ranar 2 ga wannan watan Augusta aka harba makamin rokan da ya hallaka Janar Adolphe Nshimirimana, ake gani shine ke jan ragamar harkokin tsaron ciki gida a kasar ta Burundi a kaikaice.
Janar Nshimirimana na a matsayin na hannun daman shugaba Nkurunziza, da yunkurinsa na yin tazarce karo na 3 ya haifar da mummunar zanga zanga a Burundi, lamarin da yayi sanadiyyar rasa ran mutane da dama, wasu suka tsere daga kasar.
Tuni kasashen duniya suka yi Allah wadai da zaben kasar ta Burundi, da shugaba Nkurunziza yayi nasara, inda suka bayyana shi a matsayin haramtacce.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.