Isa ga babban shafi
Najeriya

Amnesty ta bukaci Shell ya tsabtace muhallin da ya gurbata a Neja Delta

Kungiyar kare hakkin bil’adama ta Amnesty International ta ce ya zama wajibi Kamfanin Mai na Shell ya bi sahun Gwamantin Najeriya wajen magance matsalar gurbatar muhalli da ya gurbata a yankin Neja Delta.

Mutanen Ogoni sun dade suna kalubalantar Shell kan gurbata muhullinsu a yankin Neja Delta na Najeriya
Mutanen Ogoni sun dade suna kalubalantar Shell kan gurbata muhullinsu a yankin Neja Delta na Najeriya AFP PHOTO
Talla

Wannan na zuwa ne bayan shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sanar da kafa waani asusu domin daukan nauyin tsaftace yankin Ogoni a Neja Delta mai arzikin mai.

Amnesty ta bukaci kamfanin na Shell ya bi sahun gwamnatin Najeriya.

Babban jami’I a kungiyar Mark Dummet yace abin takaici ne kan yadda kamfanin Shell ya gaza wajan aiwatar da matakan da Majalisr Dinkin Duniya ta gabatar na tsafatace muhalli sakamakon kwararar man fetur a yankin.

Kungiyar ta yi marhaba da matakin da shugaba Muhamadu Buhari ya dauka, sai dai ta ce, tsarin na shugaban ba zai dauwamma ba, kuma jama’ar Ogoni za su ci gaba da zama cikin kunci matukar Kamafanin Shell bai sauya salon da ya ke amfani da shi ba wajan tsaftace muhallin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.