Kasashen duniya sun yi tir da yunkurin kisan Mbonimpa a Burundi
Kasashen Duniya sun yi Allah wadai da yunkuri kashe Pierre Claver Mbonimpa, daya daga cikin shugabanin kungiyoyin fararen hula a kasar Burundi bayan wasu mutane akan Babura sun dirka masa bindiga suka gudu.
Wallafawa ranar:
Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon ya soki yunkurin kashe jami’in, inda ya bukaci hukunta ‘Yan bindigar.
Kwamitin Sulhu na Majalisar ya bayyana kaduwarsa da harin, inda yace halin tsaro a Burundi ya tabarbare.
Jami’an diflomasiya da dama, cikin su har da Jakadun Amurka da Birtaniya da Faransa da kuma kungiyar kasahsen Afirka sun ziyarci Mbonimpa a asibiti, daya daga cikin masu sukar shugaba Pierre Nkurunziza wanda al’ummar Burundi ke adawa da matakinsa na neman wa’adin shugabanci na uku.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu