Isa ga babban shafi
Mali

An tsare mayakan jihadi a Mali

Jami’an ‘yan sandan Kasar Mali sun tsare mutane 20 da ake zargin mayakan jihadi ne kuma sun hada da faransawa biyu harma da wanda ya kitsa harin da aka kai a wani gidan cin abinci dake Bamako a watan Mayu. 

Mayakan jihadi
Mayakan jihadi KENYA-SECURITY/SOMALIA REUTERS/Feisal Omar/Files
Talla

Majiyoyin jami’an tsaro ne suka sanar da haka, inda suka ce, 'yan sandan sunyi nasarar cafke wani mutun mai suna Saouty Kouma a tsakiyar birnin Melo dake Mali , kuma shi ake zargi da kitsa harin da aka kaddamar a gidan cin abinci na La Terrasse, da ya yi sanadiyar mutuwar wani dan asalin kasar faransa daya da jami’in tsaron kasar Belgium harma da 'yan asalin kasar Mali uku, yayin da kungiyar mayakan Al-Mourabitoun suka yi ikirarin kai harin.

Har ila yau, jami’an 'yan sanda sun cafke sauran mutanen da ake zargin mayakan jihadi ne a kudancin garin Zegoua bayan sun tsallako daga kasar Ivory Cosat dake da makwabtaka da Mali yayin da tuni aka kai su birnin Bamako babban birnin Mali domin amsa tambayoyi.

A bangare guda, daya daga cikin majiyoyin jami’an tsaron ta bayyana cewa akasarin wadanda aka tsare daga kasar Mauritania suka fito kuma kadan ne daga cikinsu ‘yan kasashen Mali da Faransa.

To sai dai kawo yanzu mai magana da yawun ofishin jakadancin faransa a Mali bai ce komai ba game da kame yan asalin kasar ta Faransa.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.