Isa ga babban shafi
Najeriya-Boko Haram-Chadi

Boko Haram ta kai jerin hare hare a N'djamena da Maiduguri

Mutane 14 ne suka rasa rayukansu a wani harin kunar bakin wake da aka kai wajen hada-hada kasuwanci Jama’a a cikin birnin N’djamena na kasar Chadi, kwanaki kalilan bayan mayakan Boko haram sun dau alhakin kai harin baya da ya yi ajali mutane 38 a kasar.

Ta'adin Boko Haram a Chadi
Ta'adin Boko Haram a Chadi AFP PHOTO / STEPHANE YAS
Talla

Rahotanin sun ce maharin ya yi shiga ne irin ta mata tare da tarwatsa kansa a tsakiyar kasuwa.

Wannan kuma dai na zuwa ne a dai-dai lokaci da wasu rahotanin ke tabbatar da kai hari a tashar mota da ke garin Maiduguri na jihar Borno a safiyar yau wanda mutane 2 suka rasa rayukansu.

Ko a daran Jiya sai da aka kai hari a kauyen Ngamdu mai nisan Kilometer 100 da maiduguri inda mutane 11 suka mutu.

Kamfanin dilanci Labaran Faransa AFP ya rawaito cewa a ‘yan tsaka-kaninan mutane akalla 580 ne suka rasa rayukansu a jerin hare hare Boko Haram.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.