Isa ga babban shafi
Uganda

'Yan sandan Uganda sun kame wasu shugabannin 'yan adawan kasar

Yau Alhamis ‘yan sandan kasar Uganda sun kame wasu jagororin ‘yan adawan kasar 2, dake kalubalantar shugaba Yoweri Museveni a zaben da za ayi cikin shekara mai zuwa. An kama tsohon minista Amama Mbabazi a tsakiyar kasara, yayin da aka shugaban jam’iyyar FDC Kizza Besigye, a gidansa dake wajen Kampala, babban birnin kasar. 

Shugaban kasar Uganda, Yoweri Museveni
Shugaban kasar Uganda, Yoweri Museveni Reuters/Thomas Mukoya
Talla

An kama mutamen ne a daidai lokacin da suke shirin guidanar da gangamin yakin neman zabe.
Museveni, mai shekaru 70 a duniya, dake rike da madafun ikon kasar tun cikin shekararn 1986, ya sami amincewar jam’iyyarsa ta NRM, ya daga mata tuta a zaben na shekara mai zuwa.
Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan kasar Fred Enangan, yace an dakatar da Mbabazi daga gudanar da gamgamin siysa ne ba bisa ka’ida ba, saboda hukumar zabe bata kammala tantance shi.
Enanga yace an kama dan siyasar ne don kaucewa tashe tashen hankula, inda ya kara da cwa an kuma tsare diyar shi a yayin samamen da aka kai.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.