Isa ga babban shafi
Ghana

Ana zaman makoki a Ghana

Akalla mutane 150 aka ruwaito sun mutu sakamakon gobarar wuta a wani gidan Mai inda mutane suka fake saboda ruwan sama da aka tabka a birnin Accra. Shugaba John Dramani Mahama ya bayyana zaman makoki na kwanaki uku domin juyayi da nuna alhini ga wadanda suka mutu.

Akalla mutane 90 suka mutu sakamakon gobara da ta kona wani gidan mai
Akalla mutane 90 suka mutu sakamakon gobara da ta kona wani gidan mai REUTERS
Talla

Kungiyar agaji ta Red Cross tace sama da mutane 150 suka mutu a gobarar. Kungiyar ta ce ta kirga gawarwakin mutane 150 kuma kimanin 60 ke kwance a gadon asibiti.

Ruwan sama da aka tabka ne ya haifar da ambaliya a Accra, kuma ana hasashen gobarar ta faru ne daga wani gida da ke kusa da gidan Mai a unguwar Kwame Nkurumah inda mutane suka fake saboda ruwan sama.

Yanzu haka ana ci gaba da aikin ceto kuma a ranar Litinin ne za a fara zaman makoki kamar yadda Shugaba Dramani ya sanar a lokacin da ya ziyarci inda al’amarin ya faru.

Shugaba Dramani ya sha alwashin daukar matakai domin kaucewa sake aukuwar wannan al’amari

Ana sa ran adadin wadanda suka mutu zai karu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.