Isa ga babban shafi
Ghana

‘Yan Ghana 200 sun nemi mafaka a Brazil

Kimanin Mutanen Ghana 200 da suka je kallon wasannin gasar cin kofin duniya a Brazil suka nemi mafaka a kasar saboda rikicin addini da suka ce ya yi tsanani a Ghana. Amma Gwamnatin kasar Ghana tace Mutanen ba su da hujjar neman Mafaka a wata kasa tare da karyata ikirarinsu.

Wani Mutumin Ghana yana rike da Tutar kasar a Brazil
Wani Mutumin Ghana yana rike da Tutar kasar a Brazil Elcio Ramalho/RFI
Talla

Mutanen sun shaidawa gwamnatin Brazil cewa rikicin addini tsakanin Musulmi da wasu mabiya addinai ya yi tsanani a Ghana, abin da ya sa za su kauracewa kasar.

Mataimakin Ministan yada labaran Ghana ya fito a wata kafar Rediyo yana yin watsi da ikirarin mutanen wadanda har yanzu ba a tantance addininsu ba.

Wakilin RFI Hausa a Ghana Ridwanullah Abbas yace wannan batun ya bakantawa al’ummar Musulmi rai a kasar Ghana.

Kasar Ghana dai na daya daga cikin kasashen da ke zaman lafiya a yammacin Afrika.

02:38

Rahoto: ‘Yan Ghana 200 sun nemi mafaka a Brazil

Ridwanullah Abbas

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.