Isa ga babban shafi
Najeriya

An rantsar da Buhari da Osinbajo a Najeriya

A yau Juma’a 29 ga watan Mayu aka rantsar da Muhammadu Buhari na Jam’iyyar APC a matsayin sabon shugaban Najeriya wanda ya kada Goodluck Jonathan na Jam'iyyar PDP da ta shafe shekaru 16 tana shugabanci a kasar. Wannan ne karon farko da Jam’iyyar adawa ta kayar da Jam’iyya mai mulki a tarihin Najeriya.

Sabon Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari wanda aka rantsar a ranar 29 ga watan Mayu
Sabon Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari wanda aka rantsar a ranar 29 ga watan Mayu pmnews
Talla

Alkalin alkalai Mai shari’a Mahmud Muhammed ne ya rantsar da Buhari da mataimakinsa Farfesa Osinbajo da safiyar yau Juma'a.

Shugabannin kasashen duniya da dama ne suka halarci bikin rantsar da Buhari a Abuja fadar gwamnatin Najeriya.

John Kerry na Amurka yana cikin manyan baki da suka halarci bikin da Ministan harakokin wajen Faransa Laurent Fabius da Shugaban Afrika ta kudu Jacob zuma da Robert Mugabe na Zimbabwe.

Rahotanni sun ce an girke Sojoji a hanyoyin shiga Abuja tare da girke ‘Yan sanda a sassan birnin da suka hada da gine ginen Gwamnati.

Buhari ya taba rike mukamin Shugaban kasa a mulkin Soja shekaru 32 da suka gabata.

Sau uku Buhari yana takarar neman kujerar shugaban kasa a mulkin dimokuradiya.

Bayan lashe zaben da aka gudanar a 28 ga watan Maris, Buhari ya ce zai tabbatar da shugabanci nagari tare da bin tsari na dimokuradiya wajen tafiyar da gwamnatinsa.

Sai dai kuma Buhari zai gaji gwamnati ne a lokacin da Najeriya ke cike da matsaloli a fannoni da dama.

Babban kalubale da ke gabansa shi ne cika alkawullan da Jam’iyyarsa ta APC ta dauka na tabbatar da canji a kasar.

Buhari wanda sananne a bangaren yaki da Rashawa ya nanata cewa sabuwar gwamnatinsa ba za ta yi cudanya da rashawa ba

Domin yaki da Rashawa, tuni Buhari ya yi alkawalin bayyana kadarorinsa da duk wanda zai karbi mukami a gwamnatinsa.

Buhari wanda tsohon Soja ne ya jaddada cewa zai jagoranci Yaki da Boko Haram tare da samar da wani tsari da zai karfafawa Sojoji guiwa da magance rashawa da ta dabaibaye rundunar sojin Najeriya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.