Isa ga babban shafi
Masar

Babban Jami’in ‘Yan uwa musulmi ya rasu a gidan Yari

Wani babban jami’in kungiyar ‘yan uma Musulmi ta Muslim Brotherhood a kasar Masar, ya rasu a lokacin da ake tsare da shi tsawon shekarar guda a gidan Yari. Ma’aikatar harkokin cikin gidan kasar ta tabbatar da mutuwar jami’in mai suna Farid Isma’il mai shekaru 58.

Farid Ismail  Babban Jami'in Kungiyar 'Yan Uwa Musulmi a Masar
Farid Ismail Babban Jami'in Kungiyar 'Yan Uwa Musulmi a Masar REUTERS via telesurtv
Talla

Isma’il tsohon dan majalisar dokokin kasar ne, kuma jami’I a jam’iyyar Freedom and Justice ta hambararren shugaban kasa Mohammed Morsi, kuma ya wani asibitin birnin Alkahira ne ya rasu, bayan fama da ciwon hanta.

Cikin watan Yulin shekarar 2013 aka fara kame magoya bayan kungiyar ‘yan uwa musulmi, bayan Sojoji sun hambarar da gwamnatin Muhammad Morsi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.