Isa ga babban shafi
Nijar

Nijar ta kafa dokar yaki da safarar ‘Yan ci-rani zuwa Turai

Jamhuriyar Nijar ta kasance kasa ta farko a yammacin Afirka da ta samar da dokar safarar bakin haure a cikin kasar bayan Majalisar dokokin kasar ta jefa kuri’ar amincewa da wannan doka a jiya Litinin. Alkalumma na nuni da cewa a kowace shekara akwai mutane sama da dubu 4 da ke ratsa kasar ta yankin Agadez domin tsallaka zuwa Libya ko kuma Algeria da nufin shiga nahiyar Turai.

Laurent Fabius na ganawa da Shugaban Nijar Mahamadou Issoufou a fadarsa da ke birnin Yamai.
Laurent Fabius na ganawa da Shugaban Nijar Mahamadou Issoufou a fadarsa da ke birnin Yamai. AFP PHOTO / BOUREIMA HAMA
Talla

Hukumomin Italiya dai na ci gaba da aikin ceto rayukan bakin bakin haure a Teku wadanda ke kokarin tsallakawa zuwa Turai.

Hukumomin sun ce a bana adadin bakin hauren da ke kokarin shiga Turai zai zarce na bara inda mutane 170, 000 suka tsallaka.

Wannan kuma na zuwa ne a yayin da hukumomin Turai ke shirin daukar matakai domin magance matsalar kwararan bakin hauren.

Babbar Jami’ar Diflomasiyar Turai Federica Mogherini tace sun fito da wasu matakai 10 domin magance matsalar kwararar bakin haure da ke ci gaba da mutuwa a tekun Italiya.

Jami’ar tace a yanzu ba su da zabi illa su gaggauta daukar mataki game da matsalar bakin hauren

Matakin da kuma Nijar ta dauka a yanzu zai taimaka wajen dakile kwararar bakin hauren daga yammacin Afrika.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.