Najeriya
Sojin Najeriya sun sake ceto Mata 25 a Sambisa
Rundunar Sojin Najeriya ta sanar da ceto Karin mata da yara 25 daga hannun kungiyar Boko Haram a dajin Sambisa, tare kashe mayakan kungiyar da dama da tarwatsa sansaninsu. Daraktan yada labaran sojin, Kanal Sani Usman Kukasheka ya ce zaratan sojin Najeriya sun lalata sansanin Boko Haram bakwai a dajin Sambisa tare da jaddada aniyarsu ta kakkabe mayakan daga yankin.
Wallafawa ranar:
Talla
Kimanin mata 275 aka tafi da su zuwa asibiti domin diba lafiyarsu a Yola babban birnin Jihar Adamawa da ke makwabta da Borno inda aka yi garkuwa da Matan.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu