Isa ga babban shafi
Cote d'voire

Sojin Cote d'voire zasu gurfana a gaban kotu

Sojojin kasar Cote d’Ivoire 14 zasu gurfana a gaban Kotu sakamakon goyan bayan tsohon shugaban kasar, Laurent Gbagbo wajen kin sauka daga karagar mulki bayan ya fadi zabe

Sojin Cote d'voire
Sojin Cote d'voire
Talla

Sojojin zasu gurfana ne a gaban kotun soji, dan amsa zargin rawar da suka taka, wacce ta kai ga mutuwar mutane kusan 3,000, a tarzomar da jama’a suka  haifar bayan zabe.

Mai gabatar da karan, Ange Kessi ya shaidawa taron manema labarai cewa, cikin wadanda za’a gurfanar sun hada da likitan sojin shugaban, da kuma babban jami’in tsaron sa da ake shakkar sa a cikin kasar, Anselme Seka Yapo, da kwamadan sojin dake kare fadar shugaban kasa Dogbo Ble.

A dayan bangaren kuwa, a ranar talatar data gabata ne, kotun kasar ta daure matar tsohon shugaban, shekaru 20 a gidan yari, Sakamakon samunta da hannu a tabarbarewar tsaron kasar har, tarzomar da aka yi a shekara ta 2010, zuwa shekara ta 2011, ta yi kamari.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.