An kafa gidauniya ga iyalan Sojojin Nijar
An kaddamar da wata gidauniya a Jamhuriyyar Nijar domin tara kudaden da za a taimaka wa iyalan sojojin kasar Nijar da ke yakar Boko Haram na Najeriya. Kungiyoyin ‘yan jarida na kasar ne suka bayar da shawarar kafa gidauniyar.
Wallafawa ranar:
Ministan yada labaran Nijar Yahuza Sadisu Madobi ya ce zuwa yanzu an tara kudaden da yawansu ya kai CFA bilyan biyu.
A makon da ya gabata dubban mutanen Nijar sun fito suna zanga-zangar nuna goyon baya ga dakarun Nijar domin ba su kwarin gwuiwa ga yakin da suke yi da Mayakan Boko Haram da ke barazana ga zaman lafiya a kasar.
Ana sa ran Shugaban kasar Togo Faure Gnassingbé da takwaransa na Benin Thomas Yaya Boni za su kai ziyara kasar Nijar domin tattaunawa da Shugaba Mahammadou Issoufou game da barazanar Boko Haram.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu