Isa ga babban shafi
Nijar

Nijar na binciken harin Jirgin da ya hallaka mutane 36

Hukumomi a Jamhuriyar Nijar na ci gaba da gudanar da bincike domin tantance jirgin da ya kai harin bam tare da kashe mutane 36 a jihar Diffa. Tuni Najeriya ta musanta cewa jirgin mallakinta ne.

Wani yankin Abadam da ke kusa da garin Bosso a Nijar
Wani yankin Abadam da ke kusa da garin Bosso a Nijar EC/ECHO/Anouk Delafortrie
Talla

Jirgin ya sako bom ne a garin Abadam da ke kudu maso gabacin birnin Bosso a ranar Talata a lokacin da Jama’ar garin ke zaman makoki a harabar Masallaci, kuma al’amarin ya kashe mutane 36 tare da jikkata 27.

Har yanzu hukumomin Nijar ba su tantance inda jirgin ya fito ba, amma Ministan Shari’a kuma Kakakin gwamnati Maroua Amadou ya ce gwamnatin Nijar ta kaddamar da bincike.

Gwamnatin kasar ta jajantawa iyalan wadanda suka mutu.

Mumuni Lamido Haruna dan majalisar dokokin jamhuriyar Nijar da ke wakiltar yankin da lamarin ya faru, ya shaidawa RFI Hausa cewa yanzu haka suna jiran gwamnati ta sanar da al’ummar kasar halin da ake ciki game da Jirgin.

Wannan al’amarin dai na zuwa ne a yayin da gwamnatin kasar ta jagoranci zanga-zanga domin adawa da ayyukan Mayakan Boko Haram na Najeriya da ke yi wa Nijar barazana a yankin Diffa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.