Isa ga babban shafi
Najeriya

An yi wa Boko Haram luguden wuta da jiragen sama

Dakarun Sojan saman Najeriya sun yi wa Boko Haram luguden wuta a Gwoza da wasu yankunan da Mayakan suka kwace. A cikin wata sanarwa Rundunar Sojin tace har da dajin Sambisa aka yi wa ruwan wuta inda Boko Haram ta kafa sansani.

Sojojin Kamaru sun fatattaki Mayakan Boko Haram a Waza
Sojojin Kamaru sun fatattaki Mayakan Boko Haram a Waza REUTERS
Talla

Sanarwar da Janar Chris Olukolade ya sanya wa hannu tace an yi wa Boko Haram ruwan wuta a Gwoza cikin nasara tare da kashe mayakan da dama.

Mike Omeari Daraktan yada labaru a cibiyar yaki da ta’addanci, ya shaidawa RFI Hausa cewa Sojojin Najeriya sun kwato garuruwa da dama.

Omeari ya ce Sojojin sun kwato garuruwa 10 daga hannun Boko Haram da suka hada da Minchika a Jihar Adamawa.

A watan Yuli ne Boko Haram ta kwace garin Gwoza inda Shugaban kungiyar Abubakar Shekau ya fara ayyana kafa sabuwar daula bayan kwace garin. Sai dai babu tabbas ko akwai fararen hula cikin wadanda hare hare jiragen sama suka kashe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.