Isa ga babban shafi
Najeriya

INEC ta kare matakin dage zaben Najeriya

Hukumar Zaben Najeriya ta kare matakin da ta dauka na dage zaben kasar har zuwa 28 ga watan Maris sabanin ranar 14 ga watan Fabrairu kamar yadda aka tsara da farko. Shugaban hukumar Farfesa Attahiru Jega babu wanda ya tilasta wa hukumar ta dage zaben illa sun dauki matakin ne saboda dalilai na tsaro.

Shugaban Hukumar Zabe a Najeriya Farfesa Attahiru Jega
Shugaban Hukumar Zabe a Najeriya Farfesa Attahiru Jega RFI/Bashir
Talla

Jega ya ce INEC ta dauki matakin ne sakamakon shawarar da hafsoshin tsaron kasar suka bayar cewar ba za su iya samar da tsaro ba saboda jami’ansu na can suna aikin murkushe kungiyar Boko Haram a yankin arewa ma so gabashin kasar.

01:08

Sauti: Shugaban Hukumar Zabe Farfesa Attahiru Jega

Bashir Ibrahim Idris

Jega ya bayyana fargaba ga makomar Jami’an hukumar zabe idan har suka amince a gudanar da zaben a ranar 14 ga watan Fabrairu.

Wannan ya haifar da cece kuce a fadin kasar da ma duniya baki daya inda kasar `Amurka ta nuna damuwar ta kan lamarin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.