Amurka ta la’anci yunkurin juyin mulki a Gambia
Gwamnatin kasar Amurka ta yi Allah wadai da yunkurin juyin mulki a kasar Gambia tare da yin kira ga Amurkawa su kauracewa babban birnin kasar har sai an samu kwanciyar hankali. Amurka ta kuma yi kira ga bangarorin Gambia su kujewa rikici a cikin kasar.
Wallafawa ranar:
Ofishin jekadancin Amurka a Gambia ya fadi a cikin wata sanarwa cewa zai ci gaba da lura da halin da ake ciki a kasar tare da yin kira ga Amurkawa su kauracewa babban birnin kasar Banjul.
A ranar Talata ne aka yi kokarin murkushe wani yunkurin juyin mulki da wasu gungun Sojojin Gambia suka so kifar da gwamnatin Yahya Jammeh wanda ke ziyara a Dubai.
Rahotanni daga Gambia sun ce an cafke mutane uku da ake zargi.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu