Isa ga babban shafi
Kamaru-Najeriya

Kamaru ta yi wa Boko Haram ruwan wuta da jiragen sama

Hukumomi a kasar Kamaru sun yi amfani da jiragen yaki domin kai hari kan mayakan kungiyar Boko Haram da ke ci gaba da tabka ta’asa a kauyukan da ke kan iyakan kasar da Najeriya. Rahotanni sun ce Mayakan Boko Haram sama da 40 aka kashe.

Sojojin Kamaru  da ke yaki da Mayakan Boko Haram a arewacin kasar
Sojojin Kamaru da ke yaki da Mayakan Boko Haram a arewacin kasar Reuters
Talla

Wannan ne karon farko da kasar Kamaru ta fara amfani da Jiragen Yaki kan Mayakan Boko Haram.

Ministan sadarwa na Kamaru ya ce an kori Mayakan daga sansanin Sojoji da suka kwace a Assighasia.

A dan tsakanin nan mayakan Boko Haram na Najeriya sun kutsa kai kauyukan Kamaru da suka hada da Makari da Amchide da Limani inda suke kashe na kashewa tare da sace abinci da dukiyar jama’a.

Gwamnatin Kamaru ta ce ‘yan Boko Haram akalla 41 aka kashe, wasu na hannu wasu kuma sun ranta a na kare.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.