An bude sabuwar makabartar Ebola a Liberia
Gwamnatin kasar Liberia ta bude sabuwar Makabarta ta musamman domin Jana’izar mamatan cutar Ebola a birnin Monrovia. Wannan na cikin matakan da gwamnatin kasar ta dauka domin dakile yaduwar cutar da ke kisa cikin hanzari.
Wallafawa ranar:
Hukumar Lafiya ta duniya WHO ta fitar da sabon alkaluman mamata sakamakon cutar Ebola a yammacin Afrika, inda ta ke cewa mamata sakamakon cutar sun kai 7,842.
Mamatan na daga cikin mutane sama da dubu 20 da aka gwada suna da cutar a kasashen Guinea da Liberia da Saliyo.
Hukumar tace baya ga wadannan kasashe an kuma samu mamata shida a kasar Mali, guda a Amurka sannan kuma 8 a Najeriya.
A kasar Liberia, mutane kimanin 3,500 suka mutu sakamakon Ebola.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu